‘Yan sanda sun ceto mutane takwas da aka sace a Edo.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Edo ta bayyana cewa jami’anta sun ceto mutane takwas da wasu ‘yan bindiga suka sace a hanyar Auchi zuwa Benin.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da masu garkuwa da mutane suka tare hanyar, suka sace fasinjoji bakwai, lamarin da ya jawo ɗumbin firgici ga masu tafiya a yankin.
Kakakin rundunar, SP Chidi Nwabuzor, ya ce da zarar ‘yan sanda suka samu rahoto, sai aka tura jami’ai da sauri zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta da masu garkuwar. A sakamakon haka, an samu nasarar ceto mutane takwas, yayin da ake ci gaba da neman sauran wadanda suka tsere da su cikin daji.
Hukumar ta tabbatar da cewa bincike yana ci gaba domin cafke wadanda suka aikata laifin tare da dawo da zaman lafiya a yankin.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments