Gwamnatin Kano ta musanta jita-jitar ɗaukar malamai 3,917

(Abba K Yusuf)

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ba gaskiya ba ne rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa gwamnati na shirin ɗaukar malamai 3,917 a karkashin wani shiri mai suna Kano State Government Basic Education Teachers Mapping and Recruitment Plan (2025–2028).

A wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi, ya fitar a ranar Litinin, ya ce labarin bai da tushe balantana makama karya ce tsagwaronta.

Ya bayyana cewa ma’aikatar ba ta taba fitar da wata sanarwa ko umarni a hukumance da ya shafi ɗaukar ma'aikata ba, don haka jama’a su yi watsi da waɗannan bayanai.

“Ma’aikatar na so ta tabbatar wa jama’a cewa ba ta fitar da wata sanarwa ta hukumance game da ɗaukar malamai ba,” in ji Abdullahi.

Ya kuma bukaci jama’a su daina yarda da duk wani bayani da ba ya fitowa daga hanyoyin gwamnati, musamman idan ya shafi batutuwan ɗaukar aiki ko sauran ayyukan gwamnati.

“Ana gargadin jama’a da su tabbatar da sahihancin kowace sanarwa kafin su ɗauka da muhimmanci, musamman idan ta shafi ɗaukar malamai,” in ji shi.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments