Kamfanin tace man fetur na Dangote ya kaddamar da sayar da tataccen man fetur dinsa a gidajen man MRS dake fadin Najeriya kan farashin naira 739 a kowace lita daya. Wannan mataki na zuwa ne a matsayin wani bangare na kokarin kamfanin na ganin man ya isa kowane sako da lungu na kasar nan domin saukakawa 'yan kasa halin matsin lamba da ake ciki na karancin man fetur da tsadar sa.
Fitacciya Ta rawaito cewa, wannan sabon farashi ya fara aiki ne nan take a gidajen man na MRS, inda aka ga dandazon motoci suna bin sahu domin sayen man wanda aka bayyana cewa yana da inganci sosai. Shugabannin kamfanonin biyu sun cimma wannan yarjejeniya ce domin tabbatar da cewa an rage radadin da jama'a ke fuskanta, tare da samar da man a koda yaushe ba tare da yankewa ba.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa shigowar man Dangote cikin kasuwa kan wannan farashi zai taimaka kwarai wajen daidaita farashin man fetur a kasar, wanda a baya-bayan nan ya yi tashin gwauron zabi. Wannan hadin gwiwa tsakanin Dangote da MRS ana kallon sa a matsayin wani babban mataki na karya ikon da wasu kalilan ke da shi a fannin shigo da mai, wanda hakan zai kawo gasa mai kyau a kasuwar man fetur ta Najeriya.
A halin yanzu, direbobi da masu amfani da ababen hawa sun nuna farin cikinsu da wannan ci gaba, inda suke fatan sauran gidajen man ma za su bi sahu wajen rage farashin su. Gudanar da wannan tsari na sayar da mai a farashi mai rahusa ana sa ran zai yi tasiri kai tsaye wajen rage kudin sufuri da kuma farashin kayan abinci a kasuwanni daban-daban dake fadin kasar nan.
0 Comments