Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kama wasu manyan yan fashi da makami biyu da ake zargi da sace mota da kuma wasu kayayyaki a Abuja, bayan samun sahihin bayanan leƙen asiri da kuma gaggawar aikin jami’an tsaro.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:15 na asuba, a ranar 29 ga Oktoba, 2025, lokacin da wasu ‘yan fashi suka kutsa wani gida da ke Karu, Abuja, inda suka kwashi kuɗi da wayoyi tare da sace motar Ford Escape mallakar wani jami’in Sojojin Sama.
Bayan samun bayanai cewa masu fashin na hanyarsu ta zuwa Kano, rundunar Anti-Kidnapping ta Kano ta tare su a kan titin Kano zuwa Zaria kusa da Salbas Filling Station. Suka yi yunkurin buɗe wuta kan jami’an tsaro, sai kuwa aka yi musayar wuta, lamarin da ya kai ga tarwatsa su tare da kama biyu daga cikinsu.
Waɗanda aka kama su ne:
Adamu Adam Abubakar, mazaunin Zoo Road, Kano
Umar Bello, mazaunin Nasarawa Dirkania, Kaduna State
Sai dai wani abokin su mai suna Dan Malam (ba a tabbatar da sunan ƙarshe ba) ya arce da bindiga da kuma wasu daga cikin kayan da suka sace.
Rundunar ta ce tana biye da shi domin Kama shi.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya jinjinawa Sashen Bincike na Sirri na Hedikwatar Ƴan Sanda ta Ƙasa bisa hadin kai da suka bayar, tare da yaba wa jami’an rundunar bisa jajircewa da kwarewar da suka nuna.
Ya kuma roƙi al’umma da su rungumi bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin kawo ƙarshen cin zarafin tsaro, yana mai tabbatarwa cewa rundunar za ta ci gaba da aiki ba tare da gajiyawa ba har sai an kamo wanda ya tsere.
0 Comments