Shugaban Ƙasa Ya Sauya Hukuncin Maryam Sanda Zuwa Shekaru 12 a Gidan Yari.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya hukuncin kisa da aka yankewa Maryam Sanda, inda yanzu za ta yi shekaru 12 a gidan yari maimakon rataya.
Sabon umarnin ya fito ne ƙarƙashin tsarin Presidential Prerogative of Mercy, wanda aka sanya hannu a kai a ranar 21 ga Oktoba, 2025.
Maryam Sanda, mai shekaru 37, an yanke mata hukuncin kisa a shekarar 2020 kan laifin kisan mijinta, Bilyaminu Bello. Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin a 2022, lamarin da ya jawo cece-kuce a fadin ƙasar nan.
Sai dai sabon takardar sassauta hukuncin da fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, ta bayyana cewa an mayar da hukunci daga rataya zuwa shekaru 12 a gidan yari, bisa la’akari da tsarin tausayawa da sassauta hukunci ga wasu fursunoni.
Wannan sauyi na cikin jerin waɗanda suka amfana da rage hukunci ko afuwa a wannan shekarar, sai dai ba a yi mata cikakkiyar afuwa ba, domin za ta ci gaba da zaman gidan yari, tare da yiwuwar ragewa nan gaba bisa kyakkyawan hali.
#MaryamSanda #Hukunci #Afuwa #ShugabanKasa #ShariarKisa #Fitacciya
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments