Boko Haram sun kai hari a Borno, sun kashe kwamandan sojoji da wasu jami’ai
Mayaƙan Boko Haram sun kai mummunan hari a ƙauyen Kashimiri da ke ƙaramar hukumar Bama, jihar Borno, inda suka kashe Kwamandan rundunar soji ta 202, tare da sojoji biyar da kuma ’yan sa-kai (Civilian JTF) guda uku.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne yayin da dakarun ke dawowa daga wani samame da suka gudanar a yankin domin fatattakar ‘yan ta’adda.
Majiyoyi sun ce an yi wa sojojin kwanton ɓauna da daddare, lamarin da ya janyo musayar wuta mai zafi wadda ta yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro da dama.
An ce sojoji da dama sun jikkata, kuma an garzaya da su zuwa asibiti domin kulawa, yayin da aka tura ƙarin dakarun tsaro zuwa yankin don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali.
Tun daga shekarar 2009, ƙungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane tare da tilasta dubban mazauna yankin barin gidajensu.
Bugu da ƙari, tun daga 2015, ta faɗaɗa hare-harenta zuwa ƙasashen Kamaru, Chadi, da Nijar, lamarin da ya haddasa asarar rayuka sama da dubun biyu a yankin tafkin Chadi.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
(Hikima Radio kano)
0 Comments