Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS) ta mika tirela ɗauke da litan man fetur 60,000 ga hukumar kula da harkokin man fetur ta tsakiya da ƙasa (NMDPRA) a Katsina, bayan kama ta yayin da ake zargin tana kan hanyar fitar da man zuwa ƙasashen waje.
Fitacciya ta rawaito cewa, jami’an hukumar ta musamman mai suna Operation Whirlwind ne suka kama tirelar mai lamba KBT 226 XA a ranar 30 ga Satumba, 2025, a kan hanyar Jibia, bayan gano cewa tana ɗauke da takardu na ƙarya da kuma rashin cikakken bayanin inda za a kai man.
A cewar sanarwar da hukumar Kwastam ta wallafa a shafinta na X a yau Litinin, an bayyana cewa mika tirelar ga hukumar NMDPRA ya gudana ne a ranar Alhamis, 7 ga Nuwamba, domin tabbatar da gaskiya da daidaito a harkokin rarraba man fetur a ƙasar.
Kwamandan rundunar Operation Whirlwind na yankin Kano, Jigawa da Katsina, Sa’ad Yahaya, wanda ya wakilci babban jami’in rundunar, Kwamishina Kola Oladeji, ya ce matakin ya nuna tsayin dakan hukumar wajen kare tattalin arzikin ƙasa da kuma hana karkatar da man da aka tanadar domin amfani a cikin gida.
A cewar mai magana da yawun hukumar a Katsina, ASP Bello Isah, wannan aiki “na nuna tsauraran matakan da hukumar Kwastam ke ɗauka domin aiwatar da umarnin gwamnati na hana fitar da man fetur ba bisa ƙa’ida ba, tare da tabbatar da cewa albarkatun man suna amfani ga ‘yan Najeriya.”
Wanda ya karɓi tirelar a madadin hukumar NMDPRA, Injiniya Abdullahi Musa, ya yaba da ƙoƙarin hukumar Kwastam wajen nuna ƙwarin gwiwa da haɗin kai tsakanin hukumomin gwamnati. Ya ce irin wannan aiki na taimakawa wajen tsaftace harkar rarraba man fetur da hana safarar shi ta ɓoye.
Hukumar Kwastam ta sake nanata aniyarta ta ci gaba da yaƙar safarar kaya ta ɓoye da duk wani nau’in cin hanci da ke barazana ga tsaron tattalin arzikin ƙasa da sahihin rarraba makamashi a Najeriya.
kuci gaba da bibiyar Fitacciya domin samun ingantattun kuma tsaftattun labarai.
0 Comments