Gwamnatin Jihar Kano da Jamhuriyar Guinea Bissau sun cimma matsaya kan ƙarfafa dangantakar abota da haɗin gwiwa, musamman a fannoni na noma, ilimi, al’adu, yawon buɗe ido da ci gaban ɗan adam.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025.
Sanarwar ta ce wannan ci gaba ya biyo bayan wata ganawa da aka yi a birnin Bissau, inda tawagar jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyyar NNPP na ƙasa, Dr. Ajuji Ahmed, ta kai ziyarar ban girma ga Shugaban ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló.
Tawagar ta wakilci Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ɓangarorin biyu suka bayyana niyyarsu ta zurfafa haɗin kai a fannonin da za su ƙarfafa samar da ayyukan yi, bunƙasa matasa da koyon sana’o’i.
Daga cikin shirye-shiryen haɗin gwiwar har da horar da matasa kan gyaran wayoyin hannu (GSM repairs), kiwon kifi, da kuma cibiyoyin sarrafa kaju da mangwaro (cashew & mango value chain) don ƙara yawan samar da aiki da bunƙasa tattalin arziki.
A cewar sanarwar, Gwamnatin Kano ta bayar da guraben karatu 50 ga ‘yan ƙasar Guinea Bissau domin su karanci Harsunan Turanci da Hausa a ɗaya daga cikin manyan makarantun jihar.
Wannan mataki na nufin ƙarfafa musayar al’adu da harshe tsakanin ƙasashen biyu, tare da ƙarfafa zumuncin da ke tsakanin al’ummomin Yammacin Afirka.
A nasa jawabin, Shugaban ƙasar Guinea Bissau, Umaro Sissoco Embaló, ya yabawa hangen nesa da jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da bayyana niyyarsa ta kai ziyara ta rama zuwa Kano.
Ya ce tuni ya umarci Ministan Tsaronsa da ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Kano domin ƙara nazarin fannonin haɗin kai.
Daga cikin tawagar Kano da ta halarci taron akwai Hajiya Amina Abdullahi (Komisina ta Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman), Hajiya Sadiya Abdu Bichi (Mai ba da shawara ta musamman), Arc. Danjuma Zarewa (tsohon Darakta Janar na Urban Beautification), da Hon. Muhammad Sani Gumel.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da gina alaƙar ƙasa da ƙasa da za ta samar da damammaki ga al’ummar Kano musamman a fannoni na ilimi, kasuwanci da musayar al’adu.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments