Gwamnatin Najeriya Na shirin Kadamar da shirin wayar Da kai akan Siya da Kuma anfani da kayan Gida (Made in Nigeria)

(shugaba Bola Ahmed Tunibu)

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na kaddamar da wata babbar kamfen ta ƙasa domin ƙarfafa amfani da kaya da ayyukan da ake ƙera a Najeriya, ƙarƙashin shirin Nigeria First.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da hakan a Legas, inda ya ce manufar ita ce rage dogaro da kaya daga ƙasashen waje tare da ƙarfafa masana’antun cikin gida.

An bayyana cewa wannan kamfen zai iya haɓaka masana’antu da kashi 6%, tare da samar da sama da aikin yi 500,000 a cikin shekaru uku masu zuwa.

Gwamnatin za ta mayar da hankali kan sassa kamar:

Gyaran tsarin siye da siyarwa na gwamnati
Ƙarfafa ƙa’idoji da inganci.

Faɗaɗa fitar da kaya

Samun rancen kuɗi

Inganta wutar lantarki da hanyoyi
Haɓaka ƙwarewa da tsaro na kayan masarufi.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments