Yin Takara Da Tunibu Kamar Kashe Kai ne a 2027 - Kashim Shatema
Ya bayyana hakan ne a yayin taron Majalisar Zartarwa ta jam’iyyar APC (NEC) karo na 15, inda ya ce "wawa ne kawai" ko kuma "dan Damfara" zai yi yunkurin tunkarar Tinubu a zabe mai zuwa.
A cikin bayanin nasa mai cike da salon ba’a, Mataimakin Shugaban Kasar ya ce:
Ba a cin zabe ta hanyar hayaniya a shafukan sada zumunta (Social Media) ko surutan banza.
Ana samun nasara ne ta hanyar hadin kai da kuma kwarewar siyasa, wanda shugaba Tinubu ke da shi a hannun sa.
Duk da cewa kowa yana da hakkin yin takara, amma dai a shirye APC take ta sake lashe zabe a 2027.
Shettima ya jaddada cewa nasarar APC a 2027 ba sa’a ba ce ko caca, illa dai sakamakon jajircewa da jagorancin da shugaba Tinubu yake samarwa kasa.
Wannan furuci dai ya tayar da kura a fagen siyasar kasar, musamman a daidai lokacin da manyan
0 Comments