Saukin Mai: 'Yan Kasuwa Sun Kafa Sun Tsare A Matatar Dangote Bayan Rage Farashi Zuwa N699
Matatar Dangote ta kara tabbatar da matsayinta na babbar cibiyar rarraba man fetur a Najeriya, bayan ta dauki matakin rage farashin man zuwa Naira 699 kan kowace lita, tare da sassauta sharadin saye daga lita miliyan 2 zuwa lita 250,000 kacal.
Fitacciya Ta rawaito cewa, wadannan sauye-sauye sun janyo hankalin 'yan kasuwar man fetur matuka, inda a yanzu ake samun fiye da manyan motocin dakon mai 1,000 da ke yin cincirindo a matatar a kullum domin saro kaya.
Kamfanin bai tsaya nan ba, ya kuma bullo da wani sabon tsarin garantin banki na kwanaki 10, wanda zai tabbatar da cewa ana samun wadatar kaya ba tare da wani tsaiko ba, matakin da ya kara karfafa gwiwar 'yan kasuwa.
Shugaban Rukunin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa babban burin kamfanin shi ne samar da makamashi mai rahusa da saukin samu ga kowane dan Najeriya, inda ya jaddada cewa aikin matatar ya fi karkata ne kan kishin kasa da bunkasar tattalin arziki fiye da neman riba zalla.
A nasu bangaren, Kungiyar IPMAN mai rike da kashi 80 na kasuwar mai a kasar, ta yi kira ga mambobinta da su rungumi matatar, tana mai bayar da tabbacin cewa wannan hadin gwiwa zai kawo karshen duk wata fargabar karancin man fetur a Najeriya.
Ziyarci Shafinmu: https://fitacciya.com.ng
0 Comments