Tinubu yayiwa Gwamnoni Barazana Akan Danne Kuddin Kananan Hukumomi

Tinubu Ga Gwamnoni: Zan Fitar Da 'Executive Order' Muddin Kuka Ci Gaba Da Dannewa Kananan Hukumomi Hakki
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sako mai karfi ga Gwamnonin Jihohi, inda ya yi barazanar rattaba hannu kan Umarnin Shugaban Kasa (Executive Order) muddin suka ki bin umarnin Kotun Koli na sakar wa kananan hukumomi kudadensu.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Shugaban ya yi wannan furuci ne cikin bacin rai a taron NEC na jam'iyyar APC, inda ya ce ya lura wasu gwamnoni na ci gaba da danne kudaden duk da hukuncin da aka yanke na ba su 'yancin cin gashin kai.

Ya ce ya zuwa yanzu yana bi da su ne a sukwane, amma idan aka kai shi bango, zai dauki matakin da zai tabbatar da cewa an cire kudin tun daga tushe an kai su inda suka dace, kuma tasirin hakan zai bayyana a rabon kudi na wata mai zuwa (FAAC).

Wannan mataki dai na nuni da cewa Shugaban ya kuduri aniyar ganin an daina wasa da dukiyar talakawa a matakin kananan hukumomi, tare da tabbatar da cewa dokar kasa ta yi aiki a kan kowa.

Ziyarci Shafinmu: https://fitacciya.com.ng

Post a Comment

0 Comments