Sojoji Sun Cafke Wani Da Dimbin Harsasai A Shingen Bincike filato.
Dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya ta 'Operation Safe Haven' (OPSH) sun samu nasarar cafke wani mutum dauke da dimbin harsasai a wani shingen bincike da ke Jihar Filato.
Fitacciya Ta rawaito cewa, sojojin sun yi kicibis da wanda ake zargin ne yayin da suke gudanar da binciken ababen hawa na yau da kullum, inda suka gano harsasan da aka boye da nufin yin safararsu zuwa inda ba a sani ba.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun tsare mutumin nan take domin gudanar da bincike, yayin da rundunar ta jaddada aniyarta na ci gaba da farautar masu safarar makamai da ke rura wutar rikici a yankin.
Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro ke kara kaimi wajen tsaftace jihar Filato daga miyagun iri da kuma tabbatar da tsaro ga matafiya da mazauna yankin.
Ziyarci Shafinmu: https://fitacciya.com.ng
0 Comments