Hisbah A Kano Ta Ce Za Ta Hukunta Mata 'Yan Kasuwa Masu Shigar Banza A Social Media

Hisbah A Kano Ta Ce Za Ta Hukunta Mata 'Yan Kasuwa Masu Shigar Banza A Social Media
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar da sabon shirin daukar mataki a kan matan da ke harkar kasuwanci a shafukan sada zumunta, wadanda ke yin shigar da ta saba wa addini da sunan tallan kaya.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Babbar Kwamandar Hisbah ta mata, Dakta Khadija Sagir Sulaiman, ta bayyana cewa hukumar ta gaji da lallashi, inda ta ce duk da ziyarar nasiha da karramawa da suka kai wa wasu mata "Attajirai" a baya, har yanzu wasu sun ki dainawa.

Ta koka kan yadda irin wannan dabi'a ta 'yan kasuwar ke bata tarbiyyar sauran mata da ke koyi da su, tana mai jaddada cewa Hisbah ba za ta zuba ido tana kallo ana saba wa addini ba.

Dakta Khadija ta kuma ja kunnen mazajen wadannan mata da su fito su nuna kishinsu wajen hana matansu bayyana tsiraici a duniya. Ta ce duk da cewa Hisbah na goyon bayan matan su nemi na kansu, dole ne a yi hakan cikin mutunta ka’idojin musulunci.

Ziyarci Shafinmu: https://fitacciya.com.ng

Post a Comment

0 Comments