Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Oyo ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Lawal Faruq, bisa zargin Bankawa tsohuwar budurwarsa bayan soyayyarsu ta mutu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a cikin barikin sojoji da ke Ibadan, babban birnin jihar, inda ake zargin Faruq ya zuba wa budurwar tasa mai sannan ya kunna mata wuta sakamakon ɓacin rai da rikicin soyayya.
Wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana a shafin sa na X cewa wanda ake zargin ya fusata bayan soyayyarsa da wadda ake zargin ta ƙare, duk da alkawarin da suka yi cewa ba za su taɓa rabuwa ba.
An ce sojoji da ke cikin barikin sun yi gaggawar ceto wadda abin ya shafa, mai suna Omolola Hassan, inda suka garzaya da ita asibiti don samun kulawa kafin daga bisani su kama wanda ake zargin.
Mai magana da yawun rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da bincike domin gano cikakken dalili da kuma tabbatar da gaskiyar al’amarin.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments