Gwamnatin Jihar Kano ta kulla sabuwar yarjejeniya da kamfanonin Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy tare da Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA), domin faɗaɗa samar da makamashi mai tsafta da araha a fadin jihar.
Mai magana da yawun Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan shugaban hukumar zuba jari ta jihar, Naziru Halliru, ne ya sanya hannu a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin taron Sabunta Makamashi na Najeriya (NERIF) 2025 da aka gudanar a Abuja.
A cewar sanarwar, IRS Green Energy za ta gina masana’anta da za ta rika samar da megawatts 600 na kayayyakin hasken rana a kowace shekara, yayin da Tricell Solar Solutions za ta kafa wadda za ta samar da megawatts 500.
Wannan mataki, a cewar gwamnatin, wani babban ci gaba ne wajen samar da makamashi mai dorewa da kuma ƙarfafa tattalin arzikin jihar Kano ta hanyar kirkire-kirkire da zuba jari.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments