Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda bakwai, sun kuma kama wasu 27 da ake zargi da hannu a laifuka daban daban, tare da kwato makamai da danyen mai a Sintiri daban daban da suka gudanar cikin sa’o’i 48 a faɗin ƙasar.
Fitacciya ta rawaito cewa, rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, inda ta ce wannan ci gaba ya biyo bayan umarnin Babban Hafsan Sojan ƙasa, Laftanal Janar Waidi Shaibu, wanda ya umurci dakarun da su ƙara matsa kaimi wajen murkushe duk wata hanyar ta’addanci da safarar danyen mai.
Sanarwar ta ce a arewa maso gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun gudanar da bincike a Anguwan Church da ke Monguno, Jihar Borno, inda suka kama mutum 12 da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin ISWAP da JAS. Haka kuma, dakarun Bataliya ta 192 sun kashe ‘yan ta’adda uku a kwanton-bauna da suka yi a kan hanyar Gwoza zuwa Limankara, inda suka kwato bindiga AK-47 da harsasai.
A Dambuwa, sojoji sun kashe wani ɗan ta’adda da ya yi ƙoƙarin shiga sansanin rundunar da sunan leƙen asiri.
A arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, dakarun Operation Enduring Peace a Jihar Kaduna sun kai samame a maboyar ‘yan ta’adda da ke Kauru, inda suka halaka biyu daga cikin su.
A Filato kuwa, an kama mutum huɗu da ake zargi da hannu a kisan wasu fararen hula a Riyom, yayin da Operation Fansan Yamma a Jihar Neja ta kashe wani ɗan leƙen asiri tare da kwato babur da waya.
Hare-haren sun bazu har zuwa kudu maso kudu, inda dakarun 2 Brigade a Jihar Akwa Ibom suka kama mutane uku da ke hakar yashi ba bisa ƙa’ida ba. A Abia kuma, Bataliya ta 144 ta gano wurin tace man sata mai ɗauke da sama da lita 1,000 na danyen mai, yayin da Brigedi ta 34 a Imo ta gano wata ma’adana a Ohaji/Egbema, inda aka kwato ganguna shida da jirgin ruwa da ake amfani da shi wajen safara.
A Jihar Delta, Bataliya ta 90 Amphibious ta kama mutum uku ciki har da wanda ya sa kayan soja na jabu, inda aka kwato kayan bogi, wayoyi da magungunan gargajiya.
Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa waɗannan hare-haren na nuna sabuwar dabarar ƙarƙashin jagorancin Laftanal Janar Shaibu wajen murkushe ta’addanci da satar mai a faɗin ƙasa.
Sanarwar Ta tabbatar wa ‘yan ƙasa cewa wannan sabon mataki yana nuni da ƙudurin gwamnati na tabbatar da tsaro da zaman lafiya, tare da roƙon jama’a da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimaka wa jami’an tsaro wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar.
kuci gaba da bibiyar Fitacciya domin samun ingantattun kuma tsaftattun labarai.
0 Comments