Rundunar Sojin Sama Ta Biya Diyyar Rayukan Da Aka Rasa A Harin Kuskure A Sokoto
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta biya diyya tare da tallafawa mutanen da harin jirgin yaki ya rutsa da su bisa kuskure a jihar Sokoto. Shugaban rundunar, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ne ya bayar da wannan tallafin kudi da kayayyaki a ranar Laraba, domin rage radadin asarar rayuka da dukiyoyi da aka samu sakamakon harin da ya faru a karshen shekarar 2024.
Fitacciya Ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Disamba, 2024, yayin da dakarun rundunar Operation Fansan Yamma suke gudanar da samame kan maboyar 'yan ta'addan Lakurawa a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa dake Karamar Hukumar Silame. Rundunar sojin saman ta bayyana cewa harin kuskure ne da aka samu yayin kokarin kakkabe bata-gari, inda aka samu asarar rayukan farar hula 13 yayin da wasu takwas suka ji rauni.
Air Vice Marshal Edward Gabkwet, wanda ya wakilci shugaban rundunar sojin saman wajen mika tallafin ga Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto, ya bayyana cewa rundunar ta dauki cikakken alhakin abin da ya faru. Rundunar ta biya diyyar dabbobi da gonaki da aka lalata, sannan ta jaddada aniyarta na kiyaye rayukan farar hula ta hanyar amfani da sabbin dabarun kiyaye afkuwar hadurra a yayin gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Gwamna Ahmad Aliyu ya yaba wa rundunar sojin saman bisa nuna kwarewa da kuma daukar alhakin gyara kuskuren da aka samu, inda ya sanar da cewa gwamnatin jiha ma ta bayar da karin tallafin kudi naira miliyan 35 ga iyalan mamata da wadanda suka ji rauni. Shugaban Karamar Hukumar Silame, Alhaji Lawalli Gittarana, wanda ya karbi tallafin a madadin jama'arsa, ya bukaci rundunar da ta ci gaba da tuntubar jama'a domin tabbatar da tsaro mai dorewa a yankin.
0 Comments