PDP ta daga lokacin tantance ‘yan takara Shugabanci Jam'iyar

(PDP Plag)

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sanar da dage aikin tantance ‘yan takara da ta shirya gudanarwa kafin babban taronta na ƙasa.

Sanarwar da Kwamitin Shirya Babban Taron Jam’iyyar (NCOC) karkashin jagorancin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya fitar ta bayyana cewa jinkirin ya biyo bayan wasu dalilai da ba a bayyana ba, kuma za a sanar da sabon lokaci a nan gaba.

Tun da farko an tsara tantancewar ta gudana ne a ranar Litinin, 28 ga Oktoba, 2025, amma yanzu an dage ta har sai an kammala shirye-shiryen da suka dace.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a cikin jam’iyyar kan shugabanci da tsarin gudanar da babban taron.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

#nacce #Fitacciya #YancinFaɗa #Kano #YanJarida #GwamnatinKano #YusufAbba #HakkokinDanAdam #FreePress #MediaFreedom #Najeriya #Democracy #YancinJarida #VoiceOfThePeople #LabaranKano #BreakingNews

Post a Comment

0 Comments