Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 10 daga cikin al’ummar Fulani sun rasa rayukansu bayan wani hari da aka kai musu a ƙauyen Tilli, da ke ƙaramar hukumar Bunza a jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa maharan sun mamaye zauren Fulani cikin dare, inda suka buɗe wuta ba tare da banbanci ba.
A cewarsa, harin na iya zama ramuwar gayya ne kan mutuwar wani ɗan sa-kai da ake zargin Fulani suka kashe a baya.
Sai dai jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa ba su da cikakken bayani kan lamarin tukuna, amma jami’an tsaro sun fara bincike domin gano musabbabin tashin hankalin.
Lamarin ya tayar da hankula a yankin, inda ake ganin idan ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, zai iya haifar da sabon rikicin tsakanin al’ummomin da ke zaune tare tun shekaru.
Wasu shugabannin al’umma sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar da tsaro da adalci ga duka ɓangarorin, tare da hana faruwar irin wannan mummunan al’amari a nan gaba.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattun labarai.
(Punch)
0 Comments