Yan Sanda Sun Kama Mutum 10 Bayan Musayar wuta da yan wata Ƙungiyar Asiri a Osun

Yan Sanda Sun Kama Mutum 10 Bayan Musayar wuta da yan wata Ƙungiyar Asiri a Osun.

(police command)

Rundunar ‘yan sanda a jihar Osun sun cafke mutum 10 da ake zargin mambobin wata ƙungiyar Asiri (cultists) ne, bayan wata musayar wuta da jami’an tsaro a yankin Osogbo da kewaye ta jihar osun.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an tsaro sun gudanar da samame ne bayan samun bayanan sirri kan wasu da ake zargi da kai hare-hare a yankin Iragbiji da Osogbo.

A yayin artabun, ‘yan sanda sun yi nasarar fatattakar masu laifin tare da kama wasu daga cikinsu da makamai.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, Yemisi Opalola, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kama mutum goma yayin da sauran suka tsere cikin daji.

Ta ce rundunar ta kwace bindigogi da sauran kayan aiki da ake amfani da su wajen aikata laifuka daban daban.

A cewarta, an fara bincike kan wadanda aka kama domin gano sauran abokan aikinsu da kuma tantance irin rawar da suke takawa a ayyukan ta’addanci.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Osun, Mohammed Umar Abba, ya yabawa jami’an da suka gudanar da aikin, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani domin taimaka wa rundunar wajen murƙushe laifuka a fadin jihar.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattun labarai.


(Punch)

Post a Comment

0 Comments