Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Hanyar Abuja Zuwa Lokoja

Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Hanyar Abuja Zuwa Lokoja

(Yan daba)


Wasu ’yan bindiga sun kai hari a hanyar Abuja zuwa Lokoja, inda suka sace fasinjoji da ke cikin wata mota kirar Homa mai ɗauke da mutane 18 a kusa da ƙauyen Aseni, kan iyakar Abuja da jihar Kogi.

Rahotanni Fitacciya sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan motar kafin su tarwatsa tayoyinta, lamarin da ya tilasta wa direban tsayawa. Nan take suka tilasta wa fasinjojin fita daga mota, sannan suka yi cikin daji da su.

Shaidun gani da ido sun ce an ji karar harbe-harbe na tsawon lokaci kafin jami’an tsaro su isa wurin.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da aka sace ko wadanda suka kubuta ba.

Wannan hari ya sake tayar da hankali kan matsalar rashin tsaro a manyan hanyoyin Najeriya, musamman a yankin Arewa, inda masu safara da fasinjoji ke yawan fuskantar barazanar sacewa.

Jama’a na kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara tsaurara matakan tsaro a hanyoyin mota domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments