’Yan Sanda Sun Kashe Ƴan Bindiga Da Dama a Zamfara, Amma Sun Rasa Jami’ai Biyar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara tabbatar da rasa jami’anta guda 5, sun kuma yi nasarar kashe wasu ’yan bindiga da dama a wata musayar wuta mai zafi da ta auku a kan babban titin Gusau Funtua.
A cewar mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, lamarin ya faru ne a yankin Gidan Giye da ke ƙaramar hukumar Tsafe, lokacin da ’yan sanda ke sintiri suka faɗa tarkon wasu ’yan bindiga da suka yi musu kwanton ɓauna.
Rahotonni sun bayyana cewa tawagar jami’an ’yan sandan da ASP John Dogara ke jagoranta, sun tsunduma cikin artabu da ’yan bindigar na tsawon lokaci, inda suka kashe da dama daga cikin yan bindigar, yayin da wasu suka tsere da raunukan a jikin su.
Sai dai, rundunar ta tabbatar da cewa jami’an ta biyar daga cikin ’yan sandan da ke bakin aiki sun rasa rayukansu yayin fafatawar.
DSP Abubakar ya ƙara da cewa an dawo da zaman lafiya a yankin, tare da tura ƙarin jami’ai domin tabbatar da tsaro ga matafiya da mazauna yankin.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments