Kungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta Ƙasa (NARD) ta bayyana cewa za ta fara yajin aikin sai-baba-ta-gani a duk fadin ƙasar nan daga ranar 1 ga watan Nuwamba, 2025, bayan cikar wa’adin kwanaki 30 da ta bai wa Gwamnatin Tarayya kan aiwatar da bukatunta.
Shugaban ƙungiyar, Dr. Mohammad Suleiman, ya ce buƙatun sun haɗa da ƙarin kashi 200 cikin ɗari a tsarin albashin likitoci (CONMESS), aiwatar da sabbin alawus-alawus, da kuma ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya cikin gaggawa domin cike gibi a asibitocin gwamnati.
Dr. Suleiman ya bayyana cewa an umurci shugabannin rassan ƙungiyar a dukkan cibiyoyi su gudanar da taron gaggawa don sanar da mambobi, tare da tabbatar da cewa yajin aikin ya gudana cikin bin doka da tsarin ƙungiya.
Kungiyar ta kuma zargi wasu jami’an gwamnati da yin makirci da kuma cin gajiyar ƙoƙarin likitoci, tana mai cewa ba za ta lamunci wannan zalunci ba, kuma za ta tsaya tsayin daka wajen kare muradun mambobinta da inganta harkar lafiya a ƙasar.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattun labarai.
0 Comments