Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna alhini kan mutuwar mutane 13 a haɗarin mota daga Gombe zuwa Kano

Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna alhini kan mutuwar mutane 13 a haɗarin mota daga Gombe zuwa Kano.
(Gov Gombe)

Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matuƙar alhininsa kan mummunan haɗarin mota da ya rutsa da fasinjojin motar Kano Line da ta tashi daga Gombe zuwa Kano, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 13 tare da jikkatar wasu biyar (5).

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnan Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya fitar a ranar Lahadi, 26 ga Oktoba 2025.

A cewar sanarwar, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana hatsarin a matsayin babban rashi mai matuƙar ciwo, ba ga iyalan mamatan kaɗai ba, har ma ga Jihar Gombe da ƙasar baki ɗaya.

Gwamnan ya mika ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, tare da roƙon Allah Ya jikansu, Ya ba jikkatattun lafiya, sannan kuma Ya kare sauran matafiya daga irin wannan masifa.

Ya kuma yi kira ga direbobi da masu ababen hawa da su kasance masu taka-tsantsan a hanya, tare da bin ƙa’idojin zirga-zirga domin rage faruwar haɗurra masu ɗaukar rayuka.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattun labarai.


Post a Comment

0 Comments