Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu mutum uku da ake zargi da satar wayoyi a yayin bikin Kano Festival of Arts and Culture (KANFEST) da aka gudanar a garin Kano.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai, inda ya ce an kama wadanda ake zargin ne yayin da jami’an tsaro ke sintiri a wajen taron domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Kiyawa ya ce an tsare mutanen a ofishin ‘yan sanda na Kwalli, kuma bincike na ci gaba da gudana a kan lamarin.
Ya kuma musanta jita-jitar da ke yawo cewa wasu ‘yan daba masu makami sun kai hari a wajen bikin, yana mai cewa “babu wani rahoton da ya tabbatar da hakan, kuma an gudanar da bikin cikin natsuwa da tsaro.”
Bikin KANFEST, wanda ke nuna kyawawan al’adun Kano da martabar masu fasaha, ya ja hankalin jama’a da dama daga sassa daban-daban na jihar.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattun labarai.
#Fitacciya #nacce #YancinFaɗa #Kano #GwamnatinKano #YusufAbba #HakkokinDanAdam #FreePress #MediaFreedom #Najeriya #Democracy #YancinJarida #VoiceOfThePeople #LabaranKano #BreakingNews #FreedomOfSpeech #PoliceArrest
0 Comments