Yan Sanda Sun Tarwatsa ƴan Fashi a Bauchi, Sun Kama Masu Laifi

Yan Sanda Sun Tarwatsa ƴan Fashi a Bauchi, Sun Kama Masu Laifi.
(police)


Rundunar ƴan sanda ta jihar Bauchi ta samu nasarar tarwatsa wani hari na ƴan fashi a garin Bauchi, tare da cafke wasu da ake zargi da hannu a harin.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa jami’an rundunar sun samu bayanan sirri kan shirin harin, inda nan da nan suka ɗauki mataki domin dakatar da shi.

A cewar SP Wakil, ƴan sanda sun isa wajen kafin ƴan fashin su aiwatar da mugun aikinsu, inda suka yi arangama da su. Ya ce an kama wasu daga cikin su yayin da wasu suka tsere da raunuka.

Rundunar ta ce an kwato wasu makamai daga hannun waɗanda ake zargi, ciki har da bindigogi da wasu kayan da ake zargin sun fito da su ne daga wajen aikata laifi.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad, ya yaba da jajircewar jami’an da suka halarci aikin, tare da yin kira ga al’umma su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani domin taimaka wa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments