Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan akalla ‘yan fashi 80 a wani faɗa da ta yi da su a yankin iyakar jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Rahotanni sun bayyana cewa artabun ya barke ne bayan da ‘yan fashin suka kai hari kan wasu ƙauyuka da ke kusa da iyakar jihar, inda jami’an tsaro suka amsa da gaggawa suka fatattake su.
Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun samu nasarar hallaka da dama daga cikin ‘yan fashin, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
An kuma kwato makamai da harsasai da dama daga hannunsu.
A cewar wani jagoran ‘yan sa-kai a yankin, sojojin da jami’an tsaro na haɗin guiwa sun yi aikin bajinta wajen dawo da zaman lafiya a yankunan da rikicin ya shafa.
“An yi faɗa mai tsanani, amma alhamdulillahi, dakarun gwamnati sun ci nasara. Sun kashe da dama daga cikin ‘yan fashin da suka addabi al’umma,” in ji shi.
Sai dai har yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da cikakken bayani game da lamarin ba, yayin da ake ci gaba da sintiri a yankunan da abin ya faru domin tabbatar da tsaro.
Masana harkokin tsaro na ganin wannan nasara na iya ƙara kwarin gwiwar rundunar wajen ci gaba da yakar ta’addanci da fashi a arewa maso yammacin ƙasar.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments