Hisbah ta damke mutum 25 bisa zargin bikin aurar jinsi ɗaya a Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mutum 25 da ake zargin suna shirya bikin aurar jinsi ɗaya a wani ɗakin taro da ke unguwar Hotoro, cikin birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar sun kai samame ne a Fatima Event Centre da ke kan hanyar Hotoro Bypass, inda suka kama maza 18 da mata 7 da ake zargin suna cikin taron.
Mataimakin kwamandan hukumar, Mujahedeen Aminudeen, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hukumar ba za ta amince da irin waɗannan abubuwan da suka sabawa doka da koyarwar addinin Musulunci ba.
“Mun samu rahoton sahihi cewa an shirya wannan biki, shi ya sa muka tura jami’anmu suka kai farmaki. Mun kama mutanen da ake zargi, kuma za mu miƙa su ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike,” in ji shi.
Aminudeen ya kuma yi kira ga jama’a su ci gaba da taimaka wa hukumar da bayanai idan sun gano wani abu da yake sabawa dokokin jihar, yana mai cewa Hisbah za ta ci gaba da kare mutunci da kimar Kano.
Wannan lamari ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke yaba wa hukumar bisa tsayuwarta kan abin da ta kira kare ɗabi’a, yayin da wasu kuma ke ganin ya kamata gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar matasa da samar da ayyukan yi.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments