Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da ta’addanci a Kano

Yan sanda sun cafke wasu da ake zargi da ta’addanci a Kano.

(police)


Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cafke wasu mutane biyu da ake zargin suna cikin wata tawagar ’yan bindiga da ke addabar yankin Shanono da kewaye.

Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an kama mutanen ne da misalin ƙarfe biyu na dare, ranar 24 ga Oktoba, bayan samun rahoton sirri daga mazauna ƙauyen Farin Ruwa da ke ƙaramar hukumar Shanono.

Kiyawa ya ce bayan samun bayanan, jami’an sintiri tare da tawagar musamman ta rundunar suka yi gaggawar isa yankin, inda suka yi nasarar cafke mutanen bayan doguwar farauta da taƙaddama da suka yi da su cikin daji.

Ya ƙara da cewa bincike ya nuna cewa waɗanda aka kama suna da alaƙa da wasu tawagar ’yan ta’adda da ke yawo tsakanin jihar Kano da Jigawa.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da ƙoƙari tare da haɗin gwiwar al’umma wajen dakile duk wani yunkurin aikata laifuka a cikin jihar.

A wani labarin kuma, ’yan sanda sun ƙarfafa matakan tsaro a yankin Barebari na ƙaramar hukumar Makoda, bayan samun rahoton sabani tsakanin manoma da makiyaya, domin tabbatar da zaman lafiya da kariyar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahotanni cikin lokaci domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments