Kungiyar Yan Fim Ta Bukaci A Saki Jarumar Khadija Mai Numfashi Da ’Yan Sanda Suka Kama.
Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Arewa (AFMAN) ta yi kira ga Hukumar ’Yan Sandan Najeriya da ta saki jarumar Khadija Mai Numfashi, wadda aka kama a Kano sannan aka tafi da ita zuwa Legas.
Wannan kiran ya fito ne ta cikin wata buɗaddiyar wasiƙar da shugaban ƙungiyar, Salisu Mohammed Officer, ya aikewa Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa (IGP) a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025.
AFMAN ta bayyana babin damuwa sosai kan yadda aka tsare jarumar bisa zargin batanci da wani Kabiru Musa daga Legas ya yi, tana mai cewa hakan ya saba wa doka da ’yancin ɗan Adam, musamman ganin jarumar ba ta kai shekara 18 ba.
Ƙungiyar ta kara da cewa Khadija marainiya ce da ke ƙarƙashin kulawar mahaifiyarta, kuma tana cikin harkar finafinai bisa tsarin ƙungiyar da cikakken jagoranci, ba bisa ganganci ko rashin hankali ba.
Saboda haka, AFMAN ta roƙi babban sufeton ’yan sanda da ya shiga tsakani cikin gaggawa domin tabbatar da an saki jarumar, tare da kareta daga duk wani abu da zai kawo mata illa ko tsoro.
An bayyana cewa a ranar Jumu’a, 24 ga Oktoba, 2025, ne jami’an ’yan sanda suka kama Khadija a Kano, inda daga bisani suka tafi da ita zuwa Legas.
Wannan na da nasaba da wani takaici da cece-kuce da ta yi a TikTok da wata abokiyar ta, Marwat Dallatu ’yar Jihar Katsina abin da ya haifar da sa hannun Kabiru Legas cikin lamari.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments