Rundunar ‘yan sandan Jihar Sokoto ta kama mutane huɗu, ciki har da wata budurwa, bisa zargin hannu a kisan wani matashi da aka ce budurwar ce ta jawo shi cikin tarko tare da abokan aikinta suka kashe shi a ƙauyen Gidan Kacha, ƙaramar hukumar Gada ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayi Ali Salisu daga ƙauyen Darnawa ne, inda budurwarsa Rukayya Amadu ta gayyace shi zuwa wani wuri a cikin dajin Dabagi da sunan za su yi ganawa ta musamman.
Sai dai daga bisani aka ce ta haɗa baki da wani saurayin nata Hamisu Ibrahim, suka yi masa fashi sannan suka kashe shi.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 4 ga watan Oktoba, 2025.
Binciken ‘yan sanda ya kuma kai ga kama wasu mutum biyu;
Lawali Abdullahi da Ibrahim Abdullahi, waɗanda ake zargin sun karɓi babur ɗin da aka sace daga wurin marigayi tare da yunƙurin sayar da shi a cikin birnin Sokoto.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ahmed Musa, ya yabawa jami’an da suka gudanar da binciken, tare da gargaɗi ga ‘yan kasuwa da masu siyan kayayyaki kamar babura da motoci, da su tabbatar da binciken mallaka kafin su saya domin kaucewa ta’ammali da masu laifi.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments