Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta bayyana cewa ta samu nasarar Kama wasu mutane da ake zargi da aikata laifuka daban-daban ciki har da fashi da makami, satar mutane da kuma safarar miyagun ƙwayoyi a wasu sassa na jihar.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Shawulu Ebenezer Dan mamman, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishin rundunar da ke Minna, babban birnin jihar.
A cewar Danmamman, jami’an rundunar sun gudanar da samame a yankuna daban-daban kamar Suleja, Bida, da Shiroro, inda suka cafke wasu daga cikin masu laifin da ake nema. Ya ce an kwato makamai, bindigogi, da miyagun ƙwayoyi a hannun su.
Kwamishinan ya ƙara da cewa bincike na ci gaba domin gano sauran abokan harkar wadanda suka tsere, yana mai tabbatar da cewa rundunar ba za ta yi sassauci ba wajen yaƙi da duk wanda ke tayar da tarzoma ko aikata laifi a jihar.
Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba da bayanai ga hukumomin tsaro domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Za mu ci gaba da aiki dare da rana domin tabbatar da cewa Jihar Neja ta zama wuri mai aminci ga kowa da kowa,” in ji kwamishinan.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments