(Gombe)
Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar da rasuwar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Col. Abdullahi Bello (rtd), tare da ɗan sandansa (orderly), Sajan Adamu Husaini, a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a ranar Juma’a.
Rahotanni sun nuna cewa haɗarin ya faru ne a hanyar Malam Sidi zuwa Gombe, yayin da marigayin ke dawowa daga wani taro da aka gudanar a Maiduguri, Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, an bayyana cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya nuna alhini da takaici bisa rasuwar kwamishinan, yana mai cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaro da haɗin gwiwar hukumomin tsaro a jihar Gombe.
Gwamnan ya ce:
“Col. Abdullahi Bello mutum ne mai kishin jihar Gombe da ƙasar baki ɗaya. Mun rasa jajirtaccen ɗan ƙasa mai jajircewa da aiki tukuru.”
An bayyana cewa za a sanar da lokacin sallar jana’izarsu daga baya bayan kammala shirye-shiryen da suka dace.
Fitacciya ta yi ta’aziyya
Fitacciya na mika ta’aziyya ga iyalan marigayan, gwamnati, da al’ummar Gombe, tare da addu’ar Allah Ya jikansu, Ya gafarta musu, Ya kuma ba iyalansu haƙuri da juriyar wannan babban rashi.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments