Uwargidan Gwamnan Katsina ta yi kiran haɗin kai domin kawar da cutar shan inna (polio)

Uwargidan Gwamnan Katsina ta yi kira da a haɗa kai domin kawar da cutar shan inna.
(Zulaihat dikko Radda)


Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, ta yi kira ga hukumomi, shugabanni da iyaye a faɗin jihar da su haɗa kai domin tabbatar da cewa an kawar da cutar shan inna (polio) daga cikin al’umma baki ɗaya.

Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai kan rigakafin cutar da aka gudanar a Katsina, inda ta jaddada cewa cutar shan inna na daga cikin manyan matsalolin da ke barazana ga lafiyar yara da ci gaban kasa.
(Katsina First lady)

“Ya zama wajibi mu haɗa ƙarfi da ƙarfi domin ganin cewa ba a sake samun wani yaro da ke fama da cutar shan inna ba a jihar Katsina da ma Najeriya baki ɗaya.

 Wannan ya zama aikin kowa da kowa  gwamnati, iyaye, da al’umma,” in ji ta.

Uwargidan ta kuma yi kira ga shugabannin addini da na gargajiya da su ci gaba da amfani da matsayinsu wajen wayar da kan jama’a domin tabbatar da cewa dukkan yara sun samu rigakafi a kan lokaci.

Ta jaddada cewa gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin lafiya na kasa da kasa za su ci gaba da tallafa wa shirin kawar da cutar domin tabbatar da lafiyar kowane ɗa a Katsina.

Post a Comment

0 Comments