‘Yan sanda sun cafke mutane 12 da ake zargi da shiga ƙungiyar asiri a Osun
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta sanar da kama mutum 12 da ake zargi da shiga ƙungiyar asiri wadda ke haddasa tarzoma da aikata laifuka a wasu yankunan jihar.
Kakakin rundunar, SP Yemisi Opalola, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta ce jami’an tsaro sun gudanar da samame a wurare daban-daban, suka kuma gano bindigogi, harsasai, da wasu kayayyakin da ake amfani da su wajen aikata laifi.
Ta ce, “Bayan samun bayanan sirri, rundunar ta kai samame a yankin Ilesa da wasu sassan Osogbo, inda aka cafke mutum 12 da ake zargi da shiga ƙungiyar asiri.
An kuma gano makamai da kayan da ake amfani da su wajen kai hare-hare.”
SP Opalola ta kara da cewa an fara gudanar da cikakken bincike domin gano sauran abokan harkar su da kuma gano tushen ƙungiyar. Ta tabbatar da cewa duk wanda aka tabbatar da laifinsa zai fuskanci hukunci mai tsanani bisa doka.
Rundunar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da bayanai ga jami’an tsaro domin taimakawa wajen kawar da irin waɗannan ƙungiyoyi masu tayar da hankula.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments