Gwamna Bago ya soke shirin kai Dalibai ƙasashen waje, ya ce za a mayar da kuɗin ga Wasu ayyuka.

(bago)


Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya sanar da soke shirin tallafin karatu na ƙasashen waje da aka tsara domin ɗalibai 1,000 daga jihar, inda ya bayyana cewa kuɗin da aka ware don hakan za a yi amfani da su wajen inganta manyan ayyukan ci gaba a gida.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake karɓar sabbin ɗalibai 809 na Jami’ar Abdulkadir Kure da ke Minna, inda ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar sake duba tsarin saboda bukatar maida hankali kan ci gaban cikin gida.

“Ba laifi ne idan shugaba ya canza shawara. Mun fara tunanin tallafin waje, amma yanzu na soke shi saboda akwai abubuwa da dama da za mu iya yi da kuɗin nan a cikin jihar,” in ji Bago.

Ya kara da cewa gwamnati za ta bayar da ilimi kyauta ga waɗannan sabbin ɗaliban jami’ar tare da gina gidaje ga malamai da ma’aikata, da kuma samar da kwasa-kwasan kimiyya da lafiya don inganta harkar ilimi a Neja.

Gwamnan ya jaddada cewa manufarsa ita ce tabbatar da cewa jarin jihar ya zauna a gida domin ci gaban jama’a da bunƙasa tattalin arziki.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments