FRSC Ta Kaddamar da Sabon Tsarin Buga Lasisin Tukin Mota Cikin Awa 24.

(road Sefety)


FRSC Ta Kaddamar da Sabon Tsarin Buga Lasisin Tukin Mota Cikin Awa 24 a Legas
Hukumar Kiyaye Hanya ta Ƙasa (FRSC) ta kaddamar da sabon tsarin buga lasisin mota cikin awa 24 a cibiyar Mini Print Farm da ke Legas, domin hanzarta aiki da kuma kawar da jinkirin da ake samu wajen fitar da lasisi a yankin Kudu maso Yamma.

Shugaban hukumar, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar duba aiki a cibiyar, inda Mataimakin Kwamanda Olawale Kareem, wanda ke kula da cibiyar, ya wakilce shi.

Ya bayyana cewa tun bayan da aka fara cikakken aiki a cibiyar, an riga an samar da sama da lasisi dubu 100,000 cikin ‘yan makonni kacal. 

Wannan, a cewarsa, ya samu ne sakamakon amfani da sabbin injunan zamani masu ƙarfi, waɗanda ke iya buga lasisi guda cikin ƙasa da daƙiƙoƙi 20.

Mohammed ya ƙara da cewa ma’aikatan FRSC suna aiki ba da rana ba dare domin tabbatar da cewa an kawar da duk wani jinkiri kafin ƙarshen mako na biyu na watan Nuwamba.

Hukumar ta ce wannan tsarin yana daga cikin matakan da take ɗauka don inganta aiki, sauƙaƙa wa jama’a, da tabbatar da cewa lasisin mota yana fitowa cikin sauri da inganci.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments