(Tunibu)
Rahoton da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar ya bayyana cewa adadin kuɗin da ‘yan Najeriya ke kashewa wajen neman jinya a ƙasashen waje ya ragu da kashi 52 cikin 100 tun bayan hawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mulki.
A cewar rahoton, daga watan Mayu 2023 zuwa Maris 2025, ‘yan Najeriya sun kashe dala miliyan 4.74 kacal wajen jinyar ƙasashen waje, idan aka kwatanta da dala miliyan 9.83 da aka kashe a watanni 22 na farko a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
CBN ta danganta wannan raguwar da tsauraran matakan kula da musayar kuɗi da gwamnatin Tinubu ta ɗauka, tare da bunƙasar cibiyoyin jinya na cikin gida waɗanda ke ƙara samun inganci da amincewar jama’a.
Masana sun ce wannan sauyi babban ci gaba ne da zai iya rage asarar kuɗaɗen ƙasa, da kuma ƙarfafa saka jari a bangaren kiwon lafiya a Najeriya matakin da zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da ingantaccen tsarin jinya ga ‘yan ƙasa.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments