Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauye a jagorancin rundunonin tsaron ƙasar domin ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya da tabbatar da ingantaccen tsari wajen kare martabar ƙasa.
A sabon sauyin, Janar Olufemi Oluyede ne ya maye gurbin Janar Christopher Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaron Ƙasar.
An kuma nada Manjo Janar W. Shaibu a matsayin sabon Babba Hafan Sojojin Kasa. yayin da Air Vice Marshall S.K. Aneke ya zama Babban Hafsan Sojin Sama, sannan Rear Admiral I. Abbas ya karɓi ragamar Babban Hafsan Sojin Ruwa.
Babban Daraktan Leken Asirin Tsaro, Manjo Janar E.A.P. Undiendeye, zai ci gaba da rike mukaminsa.
Shugaba Tinubu ya gode wa tsofaffin hafsoshin tsaro bisa jajircewa da kishin ƙasa da suka nuna a lokacin aikinsu. Haka kuma, ya umarci sabbin hafsoshin da su tabbatar sun rike wannan amana ta hanyar ƙara nuna ƙwarewa, tsantseni da haɗin kai domin ci gaba da kare zaman lafiya da tsaron ƙasar.
Sabbin nade-naden sun fara aiki nan take.
0 Comments