Majalisar wakilai ta na Nazarin kudurorin karin Jihohi 55 Da Sabbin Kananan Hukumomi 278.
Majalisar Dokoki ta Ƙasa (National Assembly) ta fara nazarin sabbin shawarwari da aka gabatar mata na yin gyare-gyare cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da kuma sabbin ƙananan hukumomi 278 a faɗin ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa an gabatar da ƙuduri 69 gaba ɗaya domin nazari, wanda ya haɗa da buƙatun ƙarin jihohi, sabbin ƙananan hukumomi, da kuma gyara wasu iyakokin jihohi da ke yanzu.
Shugaban kwamitin da ke kula da gyaran kundin tsarin mulki a Majalisar Dattawa ya bayyana cewa wannan mataki na zuwa ne bayan tattaunawa da kungiyoyin farar hula, ƙungiyoyin siyasa, da masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban na ƙasar.
Ya ce:
“Manufar wannan gyaran ita ce samar da tsarin da zai fi dacewa da jama’a, wanda zai bai wa kowanne yanki damar samun wakilci mai inganci da cigaban tattalin arziki.”
Abin Da Wannan Zai Iya Haifarwa
Masana sun bayyana cewa ƙirƙirar sabbin jihohi da ƙananan hukumomi na iya taimakawa wajen:
ƙara wakilci da kusantar gwamnati da jama’a, da kuma samar da ayyuka da dama a yankuna masu tasowa.
Sai dai kuma akwai masu ganin hakan na iya janyo ƙarin kashe kuɗaɗen gwamnati, da rikice-rikicen siyasa, musamman wajen tantance yankunan da za su amfana.
A halin yanzu, majalisar na ci gaba da nazarin ƙudurin, kafin a kai shi ga matakin sauraron ra’ayoyin jama’a.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments