Babbar Kotun Jihar Gombe dake zamanta a birnin Gombe ta yanke wa Dagacin kauyen Garin Itace, Saleh Mohammed, da wani mutum mai suna Yakubu Mohammed hukuncin kisa ta hanyar rataya. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Kereng, ya yanke wannan hukuncin ne bayan ya gamsu da hujjojin da aka gabatar dake nuna cewa mutanen biyu suna da hannu dumu-dumu a kisan wani mutum mai suna Ibrahim Mohammed.
Fitacciya Ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar 23 ga watan Agusta, 2023, a kauyen Garin Itace dake Karamar Hukumar Gombe, inda aka zargi mutanen biyu da hada baki wajen aikata wannan danyen aiki. Kotun ta bayyana cewa masu gabatar da kara sun yi nasarar tabbatar da zargin kisan kai da ake yi wa wadanda ake karar, wanda hakan ya saba wa sashi na 221 na kundin shari'ar manyan laifuka.
Yayin da yake karanta hukuncin, Mai Shari’a Kereng ya bayyana cewa shaidun da aka gabatar sun nuna cewa Dagacin ya yi amfani da ikonsa wajen tursasawa da kuma taimakawa wajen aiwatar da kisan. Wannan lamari ya janyo firgici ga mazauna yankin, musamman ganin yadda jagoran al'umma wanda ya kamata ya kare rayukan mutane ya kasance shi ne aka samu da hannu a kisan daya daga cikin mabiyansa.
Lauyoyin wadanda aka yanke wa hukuncin sun nuna rashin gamsuwarsu da matakin da kotun ta dauka, inda suka nuna alamun daukaka kara zuwa kotu ta gaba domin kalubalantar hukuncin. A daya bangaren kuma, dangin mamacin sun bayyana gamsuwarsu da yadda shari'ar ta gudana, inda suka ce hakan zai zama darasi ga masu neman tayar da zaune tsaye ko cin zarafin marasa karfi a cikin al'umma.
0 Comments