Kano: An Yi Wa Ladani Yankan Rago A Masallaci, Fusatattun Jama'a Sun Kashe Mai Laifin
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da faruwar wani mummunan al'amari a yankin Maraba da ke unguwar Hotoro a birnin Kano, inda aka yi wa wani Ladani yankan rago a cikin masallaci, lamarin da ya janyo fusatattun jama'a suka hallaka wanda ake zargin nan take.
Fitacciya Ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a safiyar yau Litinin a Masallacin Yusuf Garko, inda wanda ake zargin ya yanka makogwaron Ladanin mai suna Malam Zubairu, matakin da ya fusata mazauna yankin suka bi shi suka dauki doka a hannunsu har sai da suka kashe shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana wani sashi mai matukar tada hankali na binciken, inda ya ce jami'an tsaro sun gano makogwaron mamacin a cikin aljihun wanda ake zargin bayan an bincike shi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin, yayin da aka tura jami'ai masu yawa zuwa yankin don tabbatar da doka da oda sun dore bayan tarzomar da ta biyo bayan kisan.
0 Comments