Aikin Tinubu Ne Ke Jawo 'Yan Adawa Suna Dawowa APC — Inji Hadimin Shugaban Kasa

Tururuwar Shiga APC Ta Nuna Cewa Manufofin Tinubu Sun Karbu — Fadar Shugaban Kasa


​Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa yadda manyan 'yan siyasa da jama'a ke ta sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, babbar shaida ce cewa gyare-gyaren tattalin arziki da manufofin Shugaba Tinubu sun fara haifar da da mai ido.

Fitacciya Ta rawaito cewa, wani babban hadimin Shugaban Kasa ne ya bayyana hakan, inda ya ce 'yan Najeriya suna kara gamsuwa da alkiblar da kasar ta dosa, shi ya sa suke barin jam'iyyun adawa suna komawa APC domin bada tasu gudunmawar.

​Bayanai sun nuna cewa hadimin ya yi fatali da zargin cewa yunwa ko kwadayi ke sa mutane sauya sheka, inda ya ce hakan na nuna cewa jam'iyyar APC ta samu karbuwa ne a zukatan jama'a sakamakon jajircewar Shugaban Kasa.

Aikin Tinubu Ne Ke Jawo 'Yan Adawa Suna Dawowa APC 

​Yayin da ake ci gaba da samun masu sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki, Fadar Shugaban Kasa ta ce wannan alama ce ta nasarar manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

​Wani jami'in gwamnati ya bayyana cewa idan manufofin gwamnati ba sa aiki, da babu wanda zai so ya shigo jam'iyyar, don haka kwararowar jama'a zuwa APC tabbaci ne na cewa kasar ta kama hanyar ci gaba.

Post a Comment

0 Comments