Rikicin Yelwan Musari: Dan Majalisa Fulata Ya Kai Daukin Naira Miliyan 2 Ga Wadanda Abin Ya Shafa

Domin rage radadin asarar da aka yi sanadiyyar rikicin manoma da makiyaya, Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Birniwa, Guri da Kirikasamma, Hon. Abubakar Hassan Fulata, ya tallafa wa wadanda abin ya shafa da zunzurutun kudi har Naira Miliyan Biyu.

Fitacciya Ta rawaito cewa, dan majalisar ya mika tallafin ne yayin wata ziyarar jaje da ya kai kauyukan Yalwan Musari, Abangawa da Gishinawa da ke Jihar Jigawa, inda ya bayyana lamarin a matsayin babban tashin hankali da ke bukatar kulawa ta musamman.

Bayanai sun nuna cewa Fulata ya raba kudin ne inda ya bai wa mutanen Yalwan Musari Miliyan 1, sannan ya bai wa na Abangawa da Gishinawa Miliyan 1, tare da kira ga Hukumar NEMA da ta gaggauta kawo nata daukin.

A yayin ziyarar, al'ummar garuruwan sun nuna godiyarsu tare da rokon a samar musu da fitilun titi (Solar) don inganta tsaro, bukatarsu da dan majalisar ya yi alkawarin biya musu nan ba da dadewa ba.
Source: Guri New Media Office

Post a Comment

0 Comments