Tsoro A Kano: Jirgin Sama Ya Kauce Daga Kan Hanya A Filin Mallam Aminu

1. Jirgin Sama Ya Kauce Daga Kan Hanya A Filin Mallam Aminu
(plane)

Wani yanayi na fargaba ya lullube fasinjoji a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, bayan da wani jirgin kamfanin Flybird Aircraft ya kauce daga kan titin sauka da tashi na jiragen (Runway).

Fitacciya Ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne yayin da jirgin ke kokarin sauka, inda ya subuce zuwa cikin ciyawa.
Cikin ikon Allah, hukumomin filin jirgin sun tabbatar da cewa babu wani fasinja ko ma’aikacin jirgin da ya rasa ransa ko ya samu rauni, kuma tuni aka kwashe su lami lafiya.

2. Yaki Da 'Yan Bindiga: Tinubu Ya Amince Da Kafa 'Rundunar Tsaron Daji' A Arewa
Gwamnatin Tarayya ta dauki sabon salo wajen magance matsalar tsaro, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa rundunar 'Masu Tsaron Daji' (Forest Guards) ta musamman a Arewacin Najeriya.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Nuhu Abdullahi, wani jami'in yada manufofin gwamnati ne ya bayyana hakan, inda ya ce an kirkiri rundunar ne domin fatattakar 'yan bindiga da suka maida dazuzzukan yankin maboyarsu.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake kara samun kiraye-kiraye ga gwamnati da ta tsarkake dazuzzukan Arewa daga miyagun iri.

3. "Ba Gudu Ba Ja Da Baya": NLC Ta Ce Dole Ta Yi Zanga-zangar Tsaro A Arewa
Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta jaddada cewa babu abin da zai hana ta gudanar da zanga-zangar lumana kan tabarbarewar tsaro a ranar 17 ga watan Disamba.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana hakan ne duk da ganawar da ya yi da Gwamnan Gombe kuma Shugaban Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya.

Ajaero ya ce kisan gillar da aka yi wa wani malami a Kebbi da sauran hare-hare a Arewa sun isa hujjar cewa dole a fito a nuna damuwa ga gwamnati.

4. Jami'ar Tarayya Ta Dutse (FUD) Ta Samu Sabon Shugaba (VC)
Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, ta amince da nadin Farfesa Ahmed Muhammed Gumel a matsayin sabon Shugaban Jami’ar (Vice-Chancellor).

Fitacciya Ta rawaito cewa, nadin nasa ya biyo bayan tantancewa mai zurfi da aka yi wa 'yan takarar da suka nemi kujerar.
Ana sa ran sabon shugaban zai dora daga inda na baya ya tsaya wajen ciyar da jami'ar gaba a fannin ilimi da bincike.


5. Ribadu Da Gwamnoni Sun Halarci Bikin 'Yar Shugaban CAN A Kaduna, Sun Yi Kiran Zaman Lafiya

Babban Mashawarci kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, tare da Gwamnonin jihohi da shugabannin tsaro, sun halarci daurin auren 'yar Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa a Kaduna.

Fitacciya Ta rawaito cewa, manyan bakin sun yi amfani da wannan dama wajen kira ga al'ummar Arewa da su ci gaba da zaman lafiya da hadin kai ba tare da duba bambancin addini ba.

Taron ya samu halartar Shugaban DSS da gwamnonin Benue da Gombe, lamarin da ke nuna karfin dankon zumunci a tsakanin shugabanni.


6. Yaki Da Cin Hanci: CCB Ta Fara Bincikar Kadarorin Wasu Ministoci Da Manyan Jami'ai
Hukumar Da’a ta Ma’aikata (CCB) ta sanar da cewa ta bankado bincike a kan wasu tsoffin ministoci da manyan jami’an gwamnati na yanzu wadanda ake zargi da mallakar kadarorin da suka fi karfin albashinsu.

Fitacciya Ta rawaito cewa, hukumar tana duba takardun bayyana kadarori na jami'an ne domin tabbatar da gaskiyar abin da suka mallaka, a matsayin wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa.

Source: Daily Nigerian

Post a Comment

0 Comments