Gwamna Abba Ya Kafa Runduna Ta Musamman A Kano

Gwamna Abba Ya Kafa Runduna Ta Musamman A Kano
(Abba K Yusuf)

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin kafa wata Runduna ta Musamman domin tunkarar duk wata barazanar tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren taruwar jama'a a fadin jihar.

Fitacciya Ta rawaito cewa, Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa rundunar za ta mayar da hankali wajen gudanar da sintiri, tattara bayanan sirri da sanya ido a gidajen mai da wuraren da matafiya ke yawan haduwa.

Gwamnan ya ce an dauki wannan matakin ne na rigakafi domin dakile duk wata barazana tun kafin ta kunno kai, da kuma dawo da kwarin gwiwar al'umma kan sha'anin tsaro.


Domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, Gwamnatin Jihar Kano ta kafa sabuwar Runduna ta Musamman da za ta rika sanya ido na musamman a tashoshin mota da wuraren da jama'a ke yawan taruwa.

Wannan mataki na zuwa ne a cikin wata sanarwa da Gidan Gwamnati ya fitar a ranar Lahadi, inda aka bayyana cewa rundunar za ta yi aiki tukuru wajen tattara bayanan sirri don dakile miyagun laifuka kafin su faru.

An dora wa rundunar alhakin kula da duk wasu wurare masu rauni da ke bukatar kulawa ta musamman don kare lafiyar 'yan jihar.

Post a Comment

0 Comments