(Yar guda da mai wushirya)
Kotu ta Umurci Hisbah da Ta Daura Auren Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda Cikin Kwana 60
Kotun Majistire mai lamba 7 da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali, ta bayar da umarni ga Hukumar Hisbah ta jagoranci ɗaurin aure tsakanin Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda cikin wa’adin kwana 60 daga yau.
Kotun ta kuma umarci Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano da ya kasance mai sa ido wajen tabbatar da an gudanar da auren kamar yadda aka tanada a hukuncin kotun.
Mai Shari’a Halima Wali ta gargade su cewa, idan aka kasa aiwatar da auren cikin lokacin da kotu ta bayar, za a sake gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa rashin bin umarnin shari’a.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
0 Comments