’Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane da barayi a Kaduna, sun gano bindigogi da motoci da aka sace


Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar kama wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma barayin mota, tare da kwato manyan makamai da harsasai masu yawa a sassa daban-daban na jihar.

A cikin bayanin da rundunar ta fitar ranar Litinin, 20 ga Oktoba, 2025, kakakin rundunar ya bayyana cewa rundunar Anti-Kidnapping ta cafke wani mutum mai suna Murtala Usman ɗan shekara 28 daga ƙaramar hukumar Giwa, dauke da bindigar AK-47 sabuwa da kuma harsasai 200 a kan hanyarsa ta kai makaman zuwa sansanin ’yan bindiga a yankin Kidandan.

Murtala ya amsa cewa ya shafe watanni huɗu yana safarar makamai ga ’yan ta’adda, inda ya riga ya kai bindigogi guda huɗu a wannan lokaci.

Haka kuma, a ranar 19 ga Oktoba, 2025, ’yan sanda a Kafanchan sun kama wani Usman Shuaibu, mai shekara 28, wanda ya kai hari a wani masana’antar burodi da nufin yin fashi da makami.

A yayin arangamar, ya harbi wani mutum mai suna Mohammed Abdumumin a ƙafa, amma daga bisani aka yi nasarar kama shi tare da bindigar AK-47 da harsasai.

Bindigar da aka samu daga hannunsa an bayyana cewa ita ce wadda aka sace daga hannun wani jami’in ’yan sanda a 2019 lokacin wani hari a Asibitin Gwamnati na Kafanchan.

A ranar 16 ga Oktoba, DPO na Hunkuyi Division ya kuma gano shanu 11 da ake zargin an sace su a ƙaramar hukumar Kudan, bayan haɗin kai da jami’an sa kai na yankin.

A ranar 15 ga Oktoba, jami’an ’yan sanda daga Dan Magaji Division sun yi arangama da wasu da ake zargi da fashi a Zariya, inda suka kama mutum biyu bayan musayar wuta.

An kwato bindigar Beretta, bindigar Pump Action, da harsasai daga wurinsu. Bincike ya kai ga kama wasu karin mutane huɗu ciki har da mata biyu.

Haka kuma, a ranar 14 ga Oktoba, jami’an rundunar Anti-Kidnapping sun kama wani Yakubu Adamu daga ƙaramar hukumar Igabi, dauke da bindigar AK-47 da aka ƙera a gida (fabricated).

Bincike ya kuma kai ga gano motoci guda biyu da aka sace — duk nau’in Golf Wagon ɗaya an same shi a Kano, ɗaya kuma a Kaduna.

Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Rabi’u Muhammad, ya yaba da jajircewar jami’ansa tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba da bayanai masu inganci domin taimakawa wajen kawo ƙarshen aikata laifuka a jihar.
Ya kuma gargadi ’yan ta’adda da masu aikata laifi da su guji Kaduna, yana mai cewa yanzu jihar ta fi kasancewa cikin kwanciyar hankali da tsaro fiye da da.

Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.

Post a Comment

0 Comments