Wani lamari mai tayar da hankali ya auku a ƙaramar hukumar Gubio ta jihar Borno, inda wata matashiya ta kashe kanta bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, misalin ƙarfe 6:20 na yamma, bayan budurwar ta sha matsin lamba daga iyayenta don ta amince da auren da aka shirya mata duk kuwa da cewa tana ƙaunar wani saurayi daban.
Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Bukar Fantami Gubio, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce damuwa da matsin lambar da ta fuskanta daga iyayenta ne suka sanya ta ɗauki ranta.
Ya yi kira ga hukumomin kare haƙƙin ɗan adam da jami’an tsaro da su gudanar da bincike tare da ɗaukar matakan hana irin wannan auren dole a nan gaba.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sanda da gwamnatin jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma ba kan lamarin.
Ku cigaba da bibiyar shafin Fitacciya domin samun ingantattu kuma tsaftattattun labarai.
#Fitacciya #nacce #YancinFaɗa #Kano #GwamnatinKano #YusufAbba #HakkokinDanAdam #FreePress #MediaFreedom #Najeriya #Democracy #YancinJarida #VoiceOfThePeople #LabaranKano #BreakingNews #FreedomOfSpeech #PoliceArrest #OnlineMedia #DigitalJournalism #HakkokiDaDoka #NBC #FitacciyaUpdates
0 Comments